Connect with us

Labarai

Yadda Ta Kaya A Zaman Kotu Na Yau A Kan Shari’ar Da Ake Yi Wa Abduljabbar

Published

on

Daga Amina Tahir Muhammad

Gwamnatin Kano ce dai ta yi ƙarar Abduljabbar Kabara a gaban kotu bisa zargin kalaman da za su iya tayar da fitina da kuma yin ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.

Wata kotun shari’ar musulunci da ke Ƙofar Kudu ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Sarki Yola, ta umarci shaida na farko da ya gurfana a gabanta a ranar 17 ga Fabrairu, 2022 dangane da shari’ar Abduljabbar Nasiru Kabara.

Ana zargin Abduljabbar Kabara da yin saɓo da tunzura jama’a kamar yadda gwamnatin jihar Kano ta bayyana wa kotu.

Lauyan da ke kare Abduljabbar, ƙarƙashin jagorancin Ambali Obomeileh Muhammad SAN, ya buƙaci a dawo da shaida na farko da ya sake gurfana a gaban kotu domin yi masa tambayoyi.

Lauyan masu shigar da kara, karkashin jagorancin Barista Sa’ida Suraj SAN, ya ƙi amincewa da buƙatar, inda ya buƙaci kotun da ta janye bukatar.

“An ba su isasshen lokaci akalla makonni 4 don shiryawa a cewar lauyan gwamnati.

Sai dai alkali ya amince da buƙatar da su ka roƙa na sake gabatar da shaida na farko a gaban kotun.

An dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Fabrairu da mu ke ciki.

Ana tuhumar Abduljabbar da tuhume-tuhume guda hudu da suka shafi zagi da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a lokacin karantarwarsa, wadanda suka saɓawa sashe na 382 (b) na dokar shari’ar musulunci ta jihar Kano da aka samar a shekarar 2000.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ayya Ranakun Hutun Babbar Sallah

Published

on

Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ayyana ranakun Litinin da Talata a matsayin ranakun hutun babbar sallah.

 

Hakan ma ƙunshe ne a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar a yau Juma’a.

 

Sanarwar wadda Dakta Aishetu Ndayako sakatariyar din din din a ma’aikatar ta sanayawa hannu.

 

Ministan harkokin cikin gida Tunji Ojo ya buƙaci al’ummar musulmi da su kasance masu sadaukarwa tare da koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.

 

Ministan ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiki tukuru wajen ganin ya tsare rayuwa da lafiya da dukiyoyin al’ummar ƙasar.

 

Sannan ya buƙaci al’umma da su bayar da haɗin kai wajen ci gaban ƙasar ta yadda za a samu nasara a abubuwan da ya sa a gaba.

 

Rahotanni sun nuna cewar shugaban zai yi bikin salalrsa a jihar Legas.

Continue Reading

Labarai

Tawagar Shugaban Maniyyatan Jihar Kano Ta Isa Saudiyya

Published

on

Shugaban tawagar Alhazan Jihar Kano ya isa kasa mai tsarki domin jagoranta aikin Hajjin bana a Kasar Saudiyya.

 

Bisa managartan shirye-shirye da aiki tukuru kimanin maniyyata 3,110 ne daga jihar Kano ake sa ran zasu gabatar da aikin hajji a kasar Saudiyya.

 

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda shine Amirul Hajj na Kano tare da wasu daga cikin mukarraban Gwamnati da suka hada da shugaban hukumar Alhazan Jihar Alhaji Lamin Rabi’u Danbaffa da Shugaban majalisar dokokin Jihar Kano Hon Jibril Ismail Falgore da sauransu.

 

Ibrahim Garba wanda shine wanda yake jagorantar yan jaridu kuma mai magana da yawun mataimaki Gwamna jihar kano ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da maniyyatan sun samu wayewa domin gabatar da hajji karbabbiya.

 

Ibrahim ya kara da cewa tawagar ta samu isa kasa mai tsarki ne ta kamfanin jirgin sama na Max Air daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a ranar Asabar din nan tare da wasu daga cikin ma’aikata da sauran mutane da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da damar suje domin taimakawa musu.

 

Ibrahim Garba Shu’aibu ya ce bayan zuwan maniyyatan sun samu tagomashin samun masauki mai kyau da abinci.

 

Daga karshe ya ce gwamnatin ta shirya ma’aikatan lafiya domin kula da lafiyar maniyyatan a Kasar ta Saudiyya.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Sauke Shugaban Ƙaramar Hukuma Da Mataimakinsa

Published

on

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya dakatar da shugaban karamar hukumar Alkaleri na rikon kwarya Hon Bala Ibrahim daga bakin aiki.

Gwamnan ya tsige shugaban karamar hukumar ne tare da mataimakinsa kan dalilan da ba a bayyana ba.

Gwamnan ya tsige shugaban karamar hukumar da mataimakin na shine ta cikin wata wasikar kora mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin Jihar Ibrahim Kashim Muhammad ya fitar.

Wasikar ta umarci kantoman da mataimakinsa da su gaggauta mika harkokin shugabancin karamar hukumar ga shugaban sashin gudanarwa na karamar hukumar.

Wasikar mai dauke da kwanan watan 6 ga watan Yuni 2024 na dauke da sallamar da aka yiwa shugabannin.

Bayan fitar da takardar sakataren ya aike da ita ga babban sakatare na ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu na Jihar.
Sakataren ya korar ta fara aiki ne nan take.

 

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: