Ministan yaɗa labarai a Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya ce gwamnatin ta gano mutane 96 waɗanda ke ɗaukar nauyin mayaƙan Boko Haram a Najeriya.

Lai Mohammed wanda ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin da ya ke bayani a kan nasarorin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu a kan yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya ce akwai wasu mutane 424 da gwamnatin ta gano su na tallafa wa mayaƙan Boko Hara.

Haka kuma gwamnatin ta gano wasu kamfanoni 123 da wasu masu harkar chanjin kudi 33 da su ke da hannu a ɓangaren talafa wa mayaƙan.

Daga cikin mutanen da ake zargi akwai wasu 45 da ake gab da ƙwace kadarorinsu tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta yi namijin ƙoƙari a ɓangaren yaƙi da cin hanci da rashawa duba ga irin nasarorin da ta samu tun lokacin da su ka karɓi mulki zuwa yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: