Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun kutsa cikin sansanin ƴan sanda masu kwantar da tarzoma sun kashe uku daga ciki ttare da sace wasu.

Rahotanni sun nuna cewar ƴan bindigan sun shiga sansanin da ke Ishau a ƙaramar hukumar Paikoro ta jihar Neja.

Daily Trust ta ruwaito cewar ƴan bindigan sun ƙaddamar da hare-hare a tsakanin iyakar Neja da Kaduna.

Rundunar ƴan sandan jihar ba ta ce komai a dangane da amarin ba.

Ƴan bindiga na ci gaba da kai hare-hare wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya duk da cewar gwamnatin na bayyana matakai na kawo ƙarshensu baki ɗaya.

Jami’an ƴan sanda a jihar ba su ce komai a dangane da lamarin ba har lokacin da mu ke kammala wanan labari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: