Buhari ya bayyana hakan ne yau a Addis Ababa babban birnin ƙasar Habasha.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce za su yi kokarin tabbatar da adalci a duniya domin kawo zaman lafiya a ko ina domin samar da ci gaba a nahiyar Afrika.

Buhari ya yi wannan bayanin ne a yau Asabar a Addis Ababa babban birnin Habasha yayin da ya halarci taron kungiyar tarayyar Afrika wato AU.

Wata sanarwa da mataimakin shugaban kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar ya ce shugaba ya yaba wa Firaiminstan falasdinawa  Mohammed Shtayyeh a wajen taron da yake gudana.

Ya ce a matsayin suna shugabanni su  na yin iya kokarin su kuma za su cigaba da hakan domin tabbatar da adalci.

Shugaba Buhari ya tabbatarwa da shugaban falasdinawa cewa Najeriya za ta ci gaba da bayar da gudun mawa domin wanzar da zaman lafiya tare da ci gaba.

Sannan ya tabbatar da cewar Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan mulkin dimokaraɗiyya tare da nuna goyon bayan hakan ga gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: