Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya bai wa yan Najeriya haƙuri a bisa wahalar man fetur da aka shiga a ƴan kwanakin nan.

Shugaban kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana haka a yayin da ya halarci zauren majalisar wakilai ƙarƙashin kwamitin kula da man fetur na ƙasa a ranar Laraba.
Mele Kyari ya tabbatar wa da kwamitin cewar kamfanin zai tabbatar ya samar da litar man fetur biliyan 2.5 domin wadata ƴan ƙasar da shi.

Kamfanin ya alaƙanta wahalar man da samun wani gurbataccen man fetur wanda aka yi a watan Janairu.

Mele Kyari yace zuwa ƙarshen watan da mu ke ciki za a samar da wadataccen man fetur domin ƴan ƙasar su wadata.
Shugaban kwamitin lura da al’amuran man fetur a zauren majalisar wakilai Abdullahi Mahmood ya ce, alhakin kwamitin ne ya bibiya a dangane da halin matsin da ake ciki na man fetur a ƴan kwanakin nan.\sannan ya ce kwamitin zai yi duk mai yuwuwa wajen ganin an kawo ƙarshen ƙarancin man fetur a Najeriya baki ɗaya.