Ƴan bindigan da su ka sace mutane uku da masu aikin babbar hanyar Minna sun buƙaci a basu kuɗi naira milityan 200 kafin sakin su.

An yi garkuwa da mutane uku a ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata yayin da su ke tsaka da aiki a Lambata titin da ya tafi zuwa Izom a ƙaramar hukumar Guara ta jihar Neja.
Mutanen uku sun shafe kwanaki 19 a hannun yan bindigan, kuma daga bisani ƴan bindigan su ka buƙaci a basu naira miliyan 200 kafin sakin su kamar yadda wani da ya bayyana kansa a matsayin Dogo Gide ya bayyana.

Guda cikin mutane uku da yan bindiga su ka yi garkuwa da su ya bayyana cewar, an sace su su uku wanda su ka haɗa da Monday, da kuma Muhammad Usman da wani mai suna Chikudi.

Mutanen uku na aiki ne da kamfanin Salini kamfanin da ke aikin babbar hanyar Minna zuwa Lambata.