Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da hukumar tsaro ta NSCDC domin gurfanar da daliban Najeriya da suka kammala karatunsu a gaban kuliya, waɗanda suka ki gabatar da kansu domin yin hidimar kasa bayan kammala karatunsu.

A cewar wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a Emeka Mgbemena, babban daraktan hukumar NYSC, Manjo-Janar Shuaibu Ibrahim, ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a a yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar.

 

Shugaban ya ce sashe na 13 (1(a) da (b) ya baiwa hukumar NYSC ikon gurfanar da masu ɗaliban a gaban kotu.

 

A nasa bangaren, kwamandan hukumar NSCDC, Dr Ahmed Abubakar Audi, ya ba da tabbacin shirin NYSC na cigaba da gudanar da aikin tare.

 

Shi ma daraktan shari’a na hukumar NYSC Umar Aliyu Mohammed, kwamandan ya yi alkawarin tabbatar da cewa hadin gwiwar zai cimma manufofin da ake bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: