Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sami nasarar kama wasu mata masu ƙananan shekaru a rukunin unguwar Nassarawa ta jihar.

Mai magana da yawun hukumar Lawal Ibrahim Fagge ya tabbatarwa da Matashiya TV cewar, an kama ƴan matan ne a wuraren hokewa kamar Pikolo Joint da wani gida mai suna ICU da ke unguwar Badawa a Kano.
Hukumar ta kai sumamen ne bayan samun rahooto a kan yadda ake samun ɓata gari na ta’ammali da miyagun kwayoyi da shan shisha da sauran ayyukan ashsha a wajen.

Babban kwamandan hukumar Ustaz Haroon Ibn Sina ya ja hankalin iyaye da su dinga kula da ƴaƴansu tare da tunatar da su a kan haƙkin da ya rataya a wuyansu na kula da tarbiyya.

Sa’annan ya aike da takardar gayyata ga iyayen ƴan matan da aka kama don ganin sun zo domin tantance yaran da aka kama.
Hukumar Hisbah ta ce ba za ta lamunci yadda wasu ɓata gari ke gudanar da ayyukan ashsha a jihar ba, kuma za ta sa ƙafar wando ɗaya da duk wanda ya yi ƙokarin tsallake dokokin ta.