Hukumar Hisbah a jihar Jigawa ta fasa kwalaben giya 1,426 waɗanda ta kama a wasu kananan hukumomi biyu na jihar.

Kwamandan hukumar a Jihgawa Ibrahim Ɗahiru ne ya bayyaana hakan yau Alhamis a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce sun kama jarkokin burkutu waɗana aka haɗa a matsayin giya.

Sannan sauran giyar da aka fasa ta kwalba an samesu ne a wuraren da su ka haɗa da mahaɗar holowa, Otel, da kuma wasu wurare masu alaƙa da haka.

A ranar 3 ga watan Afrilun da mu ke ciki an kama wasu mutane 14 da kwalaben giya 177 sannan wata jarka makare da burkutu a  ƙaramar hukumar Gumel ta jihar.

Sannan sun kama kwalaben giya 1,249 da wasu kwalaben giya waɗanda babu komai a ciki guda 143 sai wata mota wanda ya ce sun kama mammalakin giyar kuma an kama su ne a Dutse babban birnin jihar.

Hukumar ta godewa mutanen jihar a bisa hadin kai da su ke bayarwa musamman wajen tabbatar da bin dokokin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: