Kungiyar Izala daya daga cikin manyan kungiyoyin addinin Islama a Najeriya ta ce shugaba Buhari take goyon baya a zaben 2019.

Shugaban kungiyar na kasa Shiekh Abdullahi Bala Lau wanda ya tabbatar wa da BBC da matakin, ya ce sun yanke shawarar ne bayan wani taro na kasa da suka gudanar.
Ya ce sun lura yadda ake fuskantar lokacin zabe mawuyaci, ya kamata a yi saitin al’ummar musulmi kan abin da ya kamata.

Bala Lau wanda a baya ya ce ya tunatar da Buhari kan halin da takawa ke ciki, a wata ganawa da suka yi a fadarsa, ya ce “sun janyo hankalin al’umma cewa a lokacin zabe mai zuwa a lura da wannan shugaba mai adalci kan irin kokarin da ya soma a sake ba shi goyon baya don ya ci gaba.”

“Allah ya kawo saukin ringigimu da tashin bama-bamai dalilin zuwan shugaba Buhari, illa dan abin da ya rage na fitintinun Allah zai kawo saukinsu.”
“Don haka akwai bukatar a sake ba shi goyon baya saboda irin kudirinsa na kulawa da tausayi da tabbatar da zaman lafiya,” in ji shi.