Connect with us

Lafiya

Yadda mata za su kaucewa kamuwa daga cutar sanyi (INFECTION) – Matashiya

Published

on

Daga Mariya Murtala            Ibrahim

Ƴan uwana mata barkanmu da wannan lokaci, da fatan muna cikin ƙoshin lafiya, ya muka ji da yanayin sanyi? Allah ya bamu wucewa lafiya amin.

bisa al ada wannan shafi na duba ne kan yadda za mu   kula da jikinmu da ma ƴaƴanmu yadda za mu ƙara shiga zuciyar mazajenmu.

Kamar yadda muka yi         magana a kan yanayin sanyi, har ma muka bada wasu hanyoyi da sinadaran da za su taimaka don gujewa        lalacewar fatarmu.

A wannan lokaci kuma za mu kawo wasu hanyoyi da za mu  bi don inganta lafiyar jikinmu da ta yaranmu har ma da mai gida idan akwai.

Kowa ya sani lokacin sanyi  yanay ne da ke taɓa lafiyar jikinmu musamman mata kamar fata, gashi, da ma wasu wurare na musamman waɗanda sanyin ke mana illa har ma ya sa a tsanemu a wasu lokutan.

 

Ga wani sinadari da za mu haɗa don saka fatarmu yin laushi maimakon bushewa.

 

Idan za mu kwanta da        daddare, ya zamnto munyi wanka sannan mu shafe     fatarmu da mai wanda yake da    laushi.

Yayin da zamu    kwanta    kuma, sai mu ɗakko mai mu    sake shafawa a tafin ƙafarmu, da kuma na hannumu.

Hakan zai sa idan kin tashi da safe ki ga fatarki ta ƙara     laushi saboda rufa da kikayi da bargo, sannan kuma yin hakan zai taimaka wajen ƙara ƙarfin gani a idanunki     uwargida.

 

Sinadari na biyu kuma, bayan kin tashi, kada ki yi wanka da sassafe, don hakan zai iya haifar miki da cutar sanyi wanda mafi yawancin mata suke ɗauke da shi a yanzu, sai ki bari sai rana ta yi ma ana kamar ƙarfe 11 zuwa 12 na rana idan kuma za ki wanka da yamma, sai ki yi da wuri kamar ƙarfe 4 kafin yamma ta yi sosai.

Da fatan za mu jarraba don gujewa kamuwa da cutar sanyi, Insha Allahu za mu kawo muku hanyoyin da ake ɗaukar cututtuka da     kuma yadda za mu kiyaye kanmu a fitowa da gaba.

 

Click to comment

Leave a Reply

Lafiya

Za A Fara Biyawa Asibitocin Najeriya Tallafin Lantarki

Published

on

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta mince da biyan tallafin wutar lantarki kaso 50 a asibitocin gwamnatin ƙasar.

 

Karamin ministan lafiya Tunji Alausa ne ya shaida haka yau Alhamis a Kaduna.

 

Ministan wanda ya je kaddamar da ayyuka a asitin tarayya na jihar, wanda aka samar da wuta mi amfani da hasken rana a bangaren wankin koda.

 

Ministan ya ce biyan tallafin lantarkin zai amfani marasa lafiyan da masu jinya.

 

Ya ce za su sauya sunan asibitocin tarayya zuwa asibitoci na musamman don baiwa kowa damar zuwa a duba shi.

 

Sannan ya roki ma’aikatan da su kwantar da hankalinsu, dangane da sace wasu likitoci wanda ya c za a kubutar da su ba da jimawa ba.

Continue Reading

Labarai

Buhari Ya Sake Roƙo ASUU Su Janye Yajin Aiki

Published

on

Yayin da kungiyar malaman jami’o’i suka shafe akalla watanni bakwai suna yajin aiki shugaba kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci su hakura su janye .

Rahoton da aka samo ya bayyana cewa, Buhari ya bayyana hakan ne a taron bikin karrama Alhaji Muhammadu Indimi, shugaban kamfanin Oriental Energy Resources Ltd a birnin Maiduguri na jihar Borno.

An gudanar da wannan babban taro ne a cikin jami’ar Maiduguri, daya daga cikin manyan makarantun Najeriya da ke garkame sakamakon yajin da ASUU keyi.

Shugaban ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa Alhaji Ibrahim Gambari, wanda ya zanta kan batutuwa da yawa da suka shafi ilimi a Najeriya.

Da yake tuna batun ASUU tare da yin tsokaci a kai, Gambari ya isar da sakon Buhari da cewa

Yana da kyau su ce wani abu game da wannan yajin aikin na ASUU saboda suna karrama Alhaji Indimi wanda aka shirya wa gagarumin biki a yau domin ci gaban ilimi mai inganci da ya kawo ba a kasar nan kadai ba.

A kan haka, yana so ya isar da kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari game da ASUU da ta janye yajin aikin da take yi, ta koma aiki.

Abangare guda, Buhari ya ce tuni tattaunawa tsakanin ASUU da gwamnati akeyi, amma duk da haka kungiyar ta ci gaba da bude makarantu.

Ya kuma koka da cewa, bai dace ASUU su ci gaba da ajiye dalibai a gida ba kasancewar abubuwa sun kasa kankama.

A cewarsa, irin wannan tsawaita wa’adin yaji na dakushe ilimi tare da kawo cikas ga ci gaban mutane.

Continue Reading

Labarai

A Shirye Muke Don Sanya Hannu Ga Makashin Hanifa – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da a shirin da take domin ganin ta yi adalci ga malamin makarantar nan, Abdulmalik Tanko da aka yankewa hukuncin kisa.

Jaridar The Guardian ta nuna Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a shirye yake domin ganin an tabbatar da adalci ga masu laifin kisan.

Babban lauyan gwamnatin Kano, Musa Lawan ya bayyana cewa wasu suna tunanin ba za a hukunta wadanda aka samu da laifin kashe Hanifa ba.

A watannin baya ake zargin wasu mutane da laifin hallaka karamar yarinya mai shekara 5. A watan Yuli ne aka tabbatar masu da laifinsu.

A ranar Alhamis, Musa Lawan ya shaidawa mutanen Kano cewa wadanda aka yankewa hukunci za su dandana kudarsu.

Kwamishinan shari’a yake cewa hukumar gidan gyaran hali za ta bayar da shaidar tabbatar da hukunci, wanda zai fito bayan wa’adin daukaka kara.

Akwai kwanaki 90 da doka ta ba wadanda ake kara da nufin su daukaka shari’a idan ba su gamsu da hukuncin da Alkalin kotun tarayya ya zantar ba.

Idan ba a daukaka kara ba, gwamna zai sa hannu, idan kuwa an koma kotu, za a saurari shari’a.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: