Siyasa
Buhari ya sauka a Kano yanzunnan Ko zai ɗaga Hannun Ganduje a Kano?

Siyasa
Kwamishina Yayi Barazana Ga Alkalai, Da Yunkurin Tayar Da Tarzoma A Kano


Kwamishinan kula da kasa a jihar Kano Adamu Aliyu Kibiya, ya yi barazana ga alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamna.

Sannan kuma ya yi alkawarin tayar da rikici ga mazauna jihar, fiye da rikicin da al’ummar makotan jihar na jihohin Kaduna da Zamfara su ke fuskanta.
Mazaunan jihohin Kaduna da Zamfara dai su na fuskantar tashin hankalin hare-hare, kisa, da kuma garkuwa da su don karbar kudin fansa daga ‘yan bindiga.Wannan hare-haren dai yana faruwa sama da shekaru 10.

Aliyu ya yi zargin cewa, da akwai yiwuwar an bai wa alkalan cin hanci da rashawa dan su yi hukuncin da ba zai yi wa jam’iyyarsa dadi ba.

Kwamishinan ya yi barzanar cewa, idan alkalan kotun su ka yi hukuncin da bai bai’wa jam’iyyarsa ta NNPP nasara ba a korafin dake gabanta, to zasu biya bashin hakan da rayuwarsu.

Jam’iyyar APC da dan takarar gwamnanta Nasiru Yusuf Gawuna dai, su na kalubalantar nasarar da gwamnan jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf ya samu a zaben da ya gabata.
Kotun sauraron kararrakin zaben dai har yanzu ba ta sanya ranar da za ta yanke hukunci a kan shari’ar ba, yayin da Aliyu Adamu ya yi wannan ikirarin lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar NNPP yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a ranar Alhamis.
Taron da aka gudanar kuma ya hadar da yin addu’a, don fatan yin nasara ga tsagin nasu a hukuncin da za a yanke.
Siyasa
Jam’iyyar NNPP Ta Kori Kwankwaso


Kwamitin zartaswa na kasa a jam’iyyar NNPP sun kori tsohon dan takarar shugabancin kasar jam’iyyar Sanata Rabiu Kwankwaso, biyo bayan kin bayyana da yayi a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.

Idan za a iya tunawa shugabanvin jam’iyyar ya dakatar da Kwankwason, a taron jam’iyyar na kasa da ya wakana ranar 29 ga watan Ogustan da ya gabata a birnin Legas.
Babban kwamitin zartarwar jam’iyyar sun nada kwamitin ladabtarwa da zasu gayyaci tsohon gwamnan domin ya kare kansa, bisa tuhumar cin amanar jam’iyya da kuma wadaka da kudin yakin neman zaben jam’iyya cikin kwanaki biyar.

Kwamitin kuma yayi gargadin cewa gaza bayyana gaban kwamitin zai janyo korar Sanata Kwankwason daga jam’iyyar, bisa la’akari da tanadin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2022 ya yi.

Saboda haka, mai rikon kwaryar sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Abdulsalam Abdulrasaq ya bayyana a cikin wani jawabi a yau Talata a birnin Legas cewa, kwamitin zartarwar jam’iyyar sun kori Kwankwason nan take, saboda kin girmama gayyatar kwamitin ladabtarwar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Abdulsalam Abdulrasaq yana sanar da hukuncin da suka dauka.
Siyasa
Jam’iyyar NNPP A Najeriya Ta Dakatar Da Kwankwaso Tsawon Watanni Shida


Kwamitin amintattu a jam’iyyar NNPP a Najeriya sun sanar da dakatar da jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga cikinta.

Jam’iyyar ta naɗa Dakta Agbo Major a matsaayin shugaban jam’iyyar na riko da wasu mukamai 19.
An dakatar da Sanata Rabi’u Kwankwaso tsawon watanni shida daga jam’iyyar.

Kamfanin dillancin labarai naa ƙasa NAN ya ruwaito cewar dakatarwar ta biyo bayan wani taro da jam’iyyar ta gudanar a jihar Legas yau Talata.

Sakatare a kwamitin amintattu na jam’iyyar Babayo Muhammed Abdullahi ya bayyanawa manema labarai cewa sun dakatar da Kwankwaso bayan zargin cin dunduniyar jamiyyar wajen taimakawa shugaba Bola Tinubu.

Haka kuma sun dakatar da shi ne bisa dokar kundin tsarin gudanarwar jam’iyyar ya tanada.
Tun tuni jam’iyyar ta zargi Sanata Kwankwaso da cin dunduniyarta, wanda ta ce ya yi amfani da su ne wajen taimakawa siyasar Shugaba Bola Tinubu na Najeriya.Kwamitin amintattu a jam’iyyar NNPP a Najeriya sun sanar da dakatar da jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga cikinta.
Jam’iyyar ta naɗa Dakta Agbo Major a matsaayin shugaban jam’iyyar na riko da wasu mukamai 19.
An dakatar da Sanata Rabi’u Kwankwaso tsawon watanni shida daga jam’iyyar.
Kamfanin dillancin labarai naa ƙasa NAN ya ruwaito cewar dakatarwar ta biyo bayan wani taro da jam’iyyar ta gudanar a jihar Legas yau Talata.
Sakatare a kwamitin amintattu na jam’iyyar Babayo Muhammed Abdullahi ya bayyanawa manema labarai cewa sun dakatar da Kwankwaso bayan zargin cin dunduniyar jamiyyar wajen taimakawa shugaba Bola Tinubu.
Haka kuma sun dakatar da shi ne bisa dokar kundin tsarin gudanarwar jam’iyyar ya tanada.
Tun tuni jam’iyyar ta zargi Sanata Kwankwaso da cin dunduniyarta, wanda ta ce ya yi amfani da su ne wajen taimakawa siyasar Shugaba Bola Tinubu na Najeriya.
-
Mu shaƙata8 months ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Al'ada4 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labaran ƙetare4 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Labarai4 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini3 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Bidiyo3 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida
-
Labarai6 months ago
Akwai Jihohi Goma Da Zaɓen Gwamna Bai Kammala Ba A Najeriya Ko Har Da Kano?
-
Girke girke5 years ago
YADDA AKE LEMON SHINKAFA