Buhari ya bayyana Kano amatsayin jihar da aka fi kaunarsa fiye da mahaifarsa Daura.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cigaba da samar da tsaro tare dasamar da hanyoyin da al’umma za su ji daɗin mulkinsa.

Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin zuwansa jihar Kano yaƙin neman zaɓensa.

Bayan godiya da ya yiwa al ummar jihar ya kuma tabbatar musu da cewar yana nan sane da abubuwan da suke buƙata, kuma zai cika dukkan alƙawuran da ya ɗauka a baya matuƙar aka sake sahale masa komawa shugabancin ƙasa karo na biyu.

Cikin zuwan shugaban ƙasa ya buɗe wasu ayyuka a jihar bayan da ya ziyarci mai martaba sarkin kano Muhammadu Sanusi ll a fadarsa.

Buhari ya bayyana Kano amatsayin jihar da aka fi kaunarsa fiye da mahaifarsa Daura.

da yawan al umma ne suka halarci taron tun daga manyan ƴan siyasa na ƙasa da ma ƙetare tare da wasu gwamnonin jihohin cikin ƙasar nan.

wani al amari da ya ke yawo shi ne batun ɗaga hannun gwamnan kanon Dakta Abdullahi Umar Ganduje a yayin yaƙin neman zaɓen, wanda ake gani tamkar shugaban baya yaƙi da rashawa ganin zargin bidiyon karbar rashawa da ake yiwa gwamnan kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: