Gwamanan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya bayyana cewar ba za a yi zaɓe a jiharsa ba matuƙar hukumar zaɓe ba ta ayyana sunan ɗan takarar jam iyyar APC ba.

Hakan ya biyo bayan ƙin fitar da ɗan takarar jam iyyar APC bayan da hukumar ta ce ba su bi tsarin fitar da ɗan takara ba.
DA dai dai lokacin da shugaban jam iyyarAPC na ƙas ya lashi takobin shigar da jam iyyar a zaɓen 2019.

Sai dai hukumar ta INEC ta bakin shugabanta na ƙasa ta ce har yanzu jam iyyar ta APC ba ta da ɗan takara a Zamfara.
