Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Siyasa

Ba’a mutuntani a tafiyar Buhari ba shi ya sa na koma Atiku

“Ba kuɗi ne a gabana ba domin kuɗi ba zai iya baka komai ba, amma a san mutum yana bayar da gudunmawa ma wani abu ne” inji Adam Zango.

Jarumin fim ɗin Hausa ya bayyana cewar ba kuɗi ne ya sa shi barin Buhari ba illa rashin kulawa da gudunmawar da yake bayarwa.

Ya ce fiye da shekara guda ana masa kiranyen komawa ɓangaren Atikun amma ya yi burus ko za a samu sauyi.

A cewar jarumi Adam Zango ba ya siyasa don cin mutuncin wani, zaman lafiya ne tsakaninsa da kowa kuma komawarsa jam iyyar PDP ba zai a ya zagi Buhari ko masoyansa ba.

kalli bayanin da ya yi

cikin wani faifan bidiyo da ya yi kuma ya wallafa a shafinsa na facebook, Adam zango ya yiwa masoyansa fatan alheri, sannan ya roƙesu da su zaɓi abinda ya nuna.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: