Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai Labaran jiha Labaran ƙasa

Mun karɓi dukkan kayan aiki daga Abuja kuma za mu fara rabasu ga ofisoshinmu na ƙananan hukumomi da ke Kano ranar Laraba – INEC

Kwamishinan zaɓe na jihar Kano Farfesa Riskuwa Arahu Shehu ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a jihar Kano.

Kwamsihinan ya bayyana cewar sun karɓi dukkanin kayan aikin da suke buƙata daga helikwatarsu wanda suka killacesu a babban bankin Najeriya CBN don basu tsaro.

Cikin jawabinsa ya ce babu wani abu da suke jira a halin yanzu, kuma nan ba da jimawa ba za su fara raba kayan ga ofisoshinsu na ƙananan hukumomi a yayin da ake sa ran gudanar da zaɓe a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Farfesa Riskuwa Arahu Shehu ya ce mun kammala kai kayan aiki marasa hatsari zuwa ƙananan hukumominmu tun katin ɗaga zaɓe, yayin da a yanzu mun kammala shirinmu tsaf don raba tsauraran kayan aikin.

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: