Tsohon ma ajin jam iyyar APC na ƙasa kuma jagoran siyasa a ƙaramar hukumar Nassarawa Dakta Bala Muhammad Gwagwarwa ya tabbatarwa da al ummar jihar Kano cewar matuƙar suka zaɓi Gwamna Ganduje tabbas za su samu tagomashi daga gwamnatin tarayya.

Cikin wata gajeriyar zantawa da Mujallar Matashiya ta yi da shi ya ce, saɓanin da aka samu da tsohon jagoransu a baya shi ne ya haddasa rashin samun abubuwan more rayuwa daga gwamnatin tarayya.

Ya ce gwamna Abdullahi umar Ganduje shi ne zai yi aiki tuƙuru ya kuma jajirce don samar da cigaba a jihar Kano.

Sannan ya shawarci al Ummar jihar Kano da su kaucewa ƴan ruɗu don zaɓar akasin jam iyyar APC tamkar koma baya ne ga jihar kano.

Sannan ya godewa ƴan jihar bisa fitar ɗango tare da zaɓar jam iyyar APC a zaɓen da ya gabata, sannan ya roƙi jama a da su fito ranar 9 ga watan uku don zaɓar gwamna Ganduje da dukkan ƴan majalisu na jam iyyar APC don cigaba da samar da ayyukan alheri a faɗin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: