DAGA RABIU SANUSI KATSINA.
Da yammacin jiya litinin ne mai girma mataimakin Gwamnan jahar Katsina QS Alh Mannir Yakubu ya karbi Alh Sani Bature Gafai Dan takarar mataimakin Gwamna a karkashin jam’iyyar PRP tare da dubban magoya bayan shi.

Alh Sani Bature Gafai a jiyan ya bayyana cewa daga yau ya watsar da takarar shi kuma ya fice daga jam’iyyar shi ta PRP ya koma jam’iyyar APC tare da dumbin magoya bayan shi inda yace “nayi hakan ne saboda naga cewa hakika Mai girma Gwamnan jahar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari da mataimakin shi QS Alh Mannir Yakubu dattawa ne Kuma masu kishin jahar katsina ne idan muka yi la’akari da irin ayyukan alkhairi da suka yima jahar mu, to duk mai kishin jahar ya zama wajibi ya mara basu baya, inda ya cigaba da cewa wannan dalillan ne suka sa na hakura da takarata ta mataimakin Gwamna na yarda Alh Mannir Yakubu ka cigaba da yima Dallatu Aminu Bello Masari mataimaki domin ku cigaba da kawo ma jahar mu cigaba”.
Daga karshe yayi godiya kwarai da gaske abisa damar mataimakin Gwamna ya basu, kuma a take ya sake jaddada ma magoya bayan shi cewa da an koma gida kowa ya cigaba da gaya ma iyalanshi cewa APC sak zaayi.

A nashi jawabin, mataimakin Gwamnan jahar katsina QS Alh Mannir Yakubu bayan yayi godiya ga Allah subahanahu wata’ala kana ya tabbatar masu da jin dadin shi matuka inda yace “Insha Allah mun Karbe ku hannu biyu biyu, ya Kara da cewa wannan ya nuna cewa Alh Sani Bature Gafai dan siyasa ne mai son cigaban al umma, ba dan siyasa bane mai kishin kanshi kadai ba, Kuma ya sake cewa mutanen Gafai ku gode ma Allah da ya azirtaku da Alh Sani Bature Gafai domin tun lokacin da na sanshi mutum ne jajirtacce kuma mai son yaga al ummar shi ta cigaba”.
