Zaben Kano: Sarkin Kano yaja hankalin masu zabe da ‘yan siyasa

Maimartaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi || yaja hankalin al’ummar jihar Kano da kuma ‘yan siyasa kan zagaye na biyu na zaben gwamnan jihar da za’a gabatar a gobe Asabar 23-03-2019, Maimartaba Sarkin yayi wannan bayanin ne a safiyar yau jumu’a a babban masallachin jumu’a na garin Kano yayin da yake jagorantar addu’ar neman zaman lafiya, ga kadan daga jawabin Sarkin.

“Duk abubuwan da aka dinga jin tsoro kafin zabe Allah yayi mana maganinsu, muna rokon Allah abubuwan da muke jin tsoro da wadanda mukeji game da zaben suma Allah yayi ma maganinsu”

“munci sa’a mun samu canje-canje acikin jami’an tsaro, an kakkame da yawa daga cikin fitinannun da suka shirya tada hankalin jama’a”

“muna kara kiran ga jami’an tsaro da su cigaba da tsayawa akan kare rayukan al’umma, dukiyarsu da mutuncinsu, kuma su cigaba da daukan matakan da suka dauka na nuna cewa babu wani wanda yafi karfin doka, kuma duk mutumin da ya zama barazana ga al’umma hukuma zata kareta”

Mai martaba sarkin ya cigaba da yin bayanai masu jan hankali dangane da zaben dake zuwa a gobe Asabar.

Saurari Cikakken Jawabin Sarkin

SHIGA NAN DOMIN YIN DOWNLOADING NA CIAKKKEN JAWABIN AKAN WAYARKA

Allah ya taimaki sarki ya karawa sarki lfy.

Basheer Sharfadi
22-03-2019.

Leave a Reply

%d bloggers like this: