Tawagar Masu sa ido na Ƙungiyar Tarayyar Turai sun tabbatar, da sanun tashin hankali da sayen ƙuri’u da tare da firgita jama’a. A lokacin gudanar da kammala zaɓen jihar kano.
Ƙungiyar ta EU ta ce, ta damu sosai kan yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC tayi da hukumomin tsaro wajen ka sa magance tashin hankali da wasu matsalolin da aka samu a lokacin d ake gudanar da zaɓen na jihar Kano.
A wani rahoton da ,ƙungiyar ta EU ta fitar cewa, jami’anta sun shaida yadda wasu wakilai suka yi katsalandan da kuma sayen kuri’u a zaben na ranar 23 ga watan Maris. Kamar yadda Rfi Hausa suka rawaito.
Sun ƙara da cewa ƙungiyar ta ce, wasu ƴan daba ɗauke da makamai su ne suka firgita jama’a tare da haifar da tarnaƙi wajen gudanar da zaɓen, wanda hakan yayi sanadin hana jami’anta da kuma ƴan jaridu gudanar da ayyukansu cikin kwancitar hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: