Magajin garin Daura dai siriki ne ga babban dogarin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Majiyar mujallar Matashiya ta tabbatar da yin garkuwa da magajin garin Daura bayan da wasu ƴan bindiga suka yi awon gaba da shi.

Da magaribar fari wasu ƴan bindiga su huɗu suka tafi da Alhaji Musa Umar Magajin garin Daura.

An ɗauke Magajin garin a mota kirar 406.

Har yanzu dai babu labarin inda yake kamar yadda wakiliyarmu ta rawaito.

Da alama dai al amarin yin garkuwa da mutane na ƙara ta azzara, ko da yake a baya bayan nan ma gwamnan jihar Zamfara Abdul aziz Yari ya bayyana cewar akwai ƴan bindiga sama da dubu 10 a ɓoye duk da luguden wutar da rundunar soji ta ce tana yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: