Cikin wata hira da Mujallar Matashiya ta yi da wani da ke Tsibiri ƙaramar hukumar Naradun ta jihar Zamfara ya shaida mana cewa, ko da ranar juma ar da ta gabata an kai muau hari tare da hallaka mutanen garin.

” An ce an kawo jami an tsaro Zamfara amma mu har yanzu ko ɗan sanda ɗaya bamu gani ba kuma an kawo mana hari ya kai sau tara babu wani mataki da aka ɗauka”.
Cikin yanayin ban tausayi yake faɗa cewar, an jikkata mutane da dama a wani hari da aka kai musu garin kwannan nan suna gab da ahan ruwa don kai Azumin watan Ramadan.

” Mun kai kukanmu har mun gaji, mun nemi a kawo mana ɗauki amma har yanzu shiru muna so ko ƴan sanda a haɗamu da su mu fatattaki ƴan bindiga a garin”.

Gwamnatin tarayya dai ta sanar cewar ta kai jami an dakarun soji don fatattakar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a garin.