Siyasa
Ba yabo ba fallasa a zangon Buhari na farko -Nasiru Zango
Alhamdulillah yau ranar rantsuwar!
Yau dai mun tsallaka next level Ina Taya Mai girma shugaban kasa Muhammad Buhari da Mai girma gwamnan Kano Dr Abdullah Umar Ganduje bisa wannan rana. Ina rokon Allah yasa gaba tafi baya yawan alkhairai domin nidai a fahimtata first level din nan talaka Bai Sami wata riba ta abin azo a gani ba, a Nigeria Koda ma maki za a bayar sai dai muce ba yabo ba fallasa, Ina magana ne akan talaka Wanda a baya yake sayen shinkafa buhu nara dubu 8 yanzu Kuma zamanin Buhari muke Saya dubu 15, kunsan dai farashin man fetur kafin zuwan Mai girma Buhari yanzu Kuma kunsan Ana wa muke samunsa, a takaice dai farashin komai ya tashi a wannan, zamani nawace kujerar Makka a baya Amma yanzu anawa ake zuwa? babu shakka dole mu gayawa Mai girma PMB cewar wallahi yunwa ta karu sosai masu cin abinci sau 3 a rana sun ragu. Musamman a Arewacin Nigeria. Amma duk da yazama dole mu jinjina maka ya mai girma shugaban kasa la ‘Akari da kokarin ka a Fannin Kan abin da yashafi Boko haram, amma kuma an sami sakacin ta’ azzarar kashe kashen mutane a Zamfara da katsina GA masifar garkuwa da mutane wacce ta fantsama a fadin kasar nan. Ya Mai girma PMB nasan watakila kana kokartawa amma mu na kasa bazamu Iya gani ba domin duk kokarin ka idan cikin mu Bai dauka ba idon mu bazai Iya gane komai ba, kasan ance yunwa Bata da hankali Kuma gaskiya ana Fama da yunwa da fatara a Arewacin Nigeria. Wani abu da yakamata Baba Buhari ya duba shine batun ministocin nan har ma da kwamandodin rundunonin tsaro gaskiya lokaci yayi da za a ce ba a tsallaka next level dasu ba, yakamata ayi sabon zubi domin ni a fahimtata ta tsaka tsaki Ina GA basu tabuka komai ba, Musamman namu na nan Arewacin Nigeria wakilcinsu Bai amfana mana komai ba, amma idan akwai me gyara a shirye nake na karbi gyara. Mai girma PMB a tarihin Nigeria tun daga 1999 zuwa yanzu ban taba ganin shugaban da talakawa suka yiwa goma ta arziki kamar ka ba, dan haka nake ganin cewar lokaci yayi da suma zasu Shana a next level, talakawa Kai har da nakasassu masu Bara a titi naga sun sayi katin nan sun kankare sun aika maka saboda a zaton su Kai ne sarkin fiton samar musu da mafita, amma gashi yawanci gwiwowinsu sun yi sanyi jikinsu yayi la’asar wasu gani suke kamar ba Buharin da suka zaba bane watakila ko anyi musu musaya. A karshe nake rokon PMB ya yi tilawar alkawurran da yayi mana kafin zabe Musamman wadanda suka shafi abinci da ilimi da tsaro, domin tabbatar dasu a next level domin a first level din nan an sami matsala. Shifa talakan Nigeria saukin kai Gare shi idan ka bashi abinci da ruwa ka inganta masa harkar lafiya ka gyara kasuwanci da makarantun da zai kai yayansa shikenan ka birge shi. A karshe nake rokon Allah yayi riko da hannun ka ya mai girma PMB Allah ya taimaki Nigeria.
Nasir Zango
Siyasa
Jam’iyyar PDP Ta Lashe Zaɓen Ƙananan Hukumomin A Jihar Akwa Ibom APC Ta Yi Watsi Da Sakamakon
Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Akwa Ibom ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi a jihar.
Hukumar ta ce jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben kujerun da aka yi a jihar.
An gudanar zaɓen ne a jiya Asabar.
Shugaban hukumar zaben ta jihar Aniede Ikoiwak ne ya sanar da sakamakon yau a ofishin hukumar da ke jihar
Ya ce jam’iyyar PDP ta lashe dukkanin kujerun ƙananan hukumomi 30 a jihar.
Yayin da jam’iyyar APC ta lashe kujerar shugaban karamar hukuma guda.
Sai dai jam’iyyar APC a jihar ta yi watsi da sakamakon wanda ta yi zargin an yi magudi a zaben.
Siyasa
Jam’iyyar NNPP Ta Tsayar Da Kuɗin Fom Ɗin Takarar Shugaban Karamar Hukumar Da Kansila
Jam’iyyar NNPP ajihar Kano ta ayyana naira 600,000 amatsayin kuɗin sayen fom ɗin takarar shugaban ƙaramar hukumar yayin da masu neman kujerar kansila za su sayi fom kan kuɗi naira 200,000.
Shugaban hukumar a jihar Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai a jihar yau Talata.
Ya ce jamiyyar na yin duk mai yuwuwa wajen ganin sun shiga zaɓen na dukkani gurbin da ake da su.
Sai dai ya buƙaci ƴan takarar da su ke riƙe da muƙamai zaɓaɓɓu ko waɗanda aka naɗa da su ajiye muƙamansu don cika sharuɗan hukumar zaɓe ta jihar Kano.
Ya ce hakan zai tosheduk wata ƙofa da za ta haifar da tazgaɗo tare da biyayya ga ƙa’ida da dokokin hukumar zaɓen
Dangane da batun naira miliyan goma matsayin kuɗin fom ɗin takara ga masu son tsayawa shugabancin ƙaramar hukuma da kuma naira miliyan biyan ga masu son tsayawa takarar kansila, shugaban jam’iyyar ya ce hukumar zaɓen ta ayyana ne domin tabbatar da cewar masu kishi da son tsayawa takarar kuma su ka cancanta ne a kai.
Shugaban ya ce jam’iyar NNPP ta mayar da hankali ne wajen harkar ilimi da talafawa matasa don su dogara da kansu.
Haka kuma jam’iyyar za ta tantance ƴan takarar a ɓangaren ilimi.
Siyasa
Gwamnan Kano Ne Ya Ɗauki Nauyin Rikicin Zanga-Zanga – Ganduje
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC a Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya zargi gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da hannu wajen ta da yamusti yayin zanga-zangar yunwa jihar.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Kano ta ce an sace tadardun zargin da ake yi masa da matarsa da dansa wanda aka shigar da kara a gaban kotu.
Ganduje ya zargi gwamnatin Kano da hannu wajen tada hargitsi don bata gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ganduje ya yi zargin yau a Abuja a wata sanarwa da saataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC ta ƙasa Edwin Olofu ta sanyawa hannu.
Ya ce sun samu bayanai na ƙarƙashin ƙasa wanda au ka gano gwamnn jihar Abba Kabir Yusuf ne ya ɗauki nauyin zanga-zangar don bata gwamnatin tarayya.
Ya ce gwamnan ya dauki nauyin rikicin wanda ya yi silar rasa rayuka da asarar dukiya.
Ya ce sun yi Alla Wadai da lamarin wanda aka yi yunkurin ruguza Kano.
Dangane da batun da gwamnatin Kano ta yi na sace takardun tuhuma da ake yiwa tsohon gwamnan Kano a babbar kotun jihar, Ganduje ya ce abin dariya ne.
-
Labarai8 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari