Gamayyar kungiyoyi daban daban ne suka ziyarci fadar shugaban kasa a ranar litinin, sakamakon karuwar rasa rayuka da ke aukuwa a jihar zamfara.
Ziyarar wadda aka gudanar bias jagorancin shugaban gamayyar kungiyoyin Usman Balarabe da matar gwamnan jihar Kaduna Asia Muhammad Ahmad, awanni 48 bayan kisan gilla da aka yiwa mutane a jihar Sokoto.
Gamayyar kungiyoyin sun nuna damuwarsu matuka ganin yadda kasha kashen rayuka ke kamari a jihar zamfara da ma wasu makotan jihar.
Sai dai shugaba muhammadu buhari ya bayyana aniyar daukar tsauraran matakai don hukunta wadan ke da hannu a ciki, tare da kawo karshen matsalar tsaro a jihar da ma kasa baki daya.