Labarai
Shugaban Mujallar Matashiya ya yi gugar zana a kan ɓata garin ƴan Jarida
Karen farauta
Bismillahirrahmanirrahim Allah ka tsaremu mugun ji da mugun gani
Babbar barazanar da ke illa cikin ruwan sanyi bai wuce yadda masu amo da kwarwa ke ƙasƙantar da kansu a gaban bayin talakawa ba.
Muddin za a cigaba a haka babu shakka babban naƙasu da koma baya na tafe cikin al umma.
Kamar yadda na ji cewa cikin rukunin mutanen da suka jajirce aka tabbatar da ƴanci a ƙasa sune tsani na huɗu da babu abinda zai yuwu sai da su, sai dai a shiga rigarsu don biyan buƙatar waɗanda ke da maiƙo a jikinsu.
Haƙiƙa akwai abubuwan ban mamaki da ban haushi wasu lokutan ma sai mutum ya kyalkyala dariya idan haushi ya ƙure ganin cewa mutanen da ke da dama sun zubar da ita suna damalmala hannu cikin bagiren da ba za su samu daraja ba bayan sun dawo ga al umma.
Ko da yake an ce hatimin nasara ya fi daraja ga mutunci amma ga masu hankali sun san cewa hakan tsantsar gangan ce da babu birkin tsayawa a daidai.
Babban abin takaici ne ganin yadda ake amfani da wasu daga cikin mutane masu daraja don biyan buƙatar wasu ko da yake akwai wasu masu zaman kansu da ake samun oganninsu a shaƙa musu naira su kuwa su tirsasa na ƙasansu don cimma burin mutane ƙalilan da za su amfanar da kansu ba al umma ba.
Sanin kowa ne yadda aka ringa yaɗa labarai na gangan tare da amfani da manyan kafafen yaɗa labarai wajen ƙirƙirar labarai ko kambama abu don cimma burin wani ɓangare a siyasa, haƙiƙa hakan illa ce babba a nan gaba.
Bari na taƙaita, abinda zai faru a ƙarshe shi ne za a samu gurɓatattun mutanen da za su hanaku cin kuɗin da kuka karɓa ko kuka kwasa, idan kuka dawo cikin mutanen kuka gujesu tun a farko ba za ku yi mutunci ba.
An ɗaukeku tamkar masu kawo wahayi amma a wannan lokaci an shiga shakku kan zantukan da kuke yaɗawa tunda idan mutum bai yi taka tsantsan ba sai ya afka mawankar Ƙuliya.
Tunda ko da a yanzu baku da mutunci da daraja a idon wancananka saboda sun san abinda kuke ƙullawa, ba wata barazana ta faɗar gaskiya da za ta tinzirasu tunda dai kun.zubar da ƙima da mutuncinku a idonsu.
Amma har yanzu ba a makara ba za a iya ɗaukar gaɓaran gyara don samun nasarar aikin a nan gaba.
Abubakar Murtala Ibrahim
28/06/2019
Labarai
Matsalar Yunwa Ya Kama Ku Magance Ba Kama Masu Zanga-zanga Ba- PDP
Jam’iyyar PDP ta Kasa ta bayyana cewa abun takaici ne yadda gwamnatin tarayya ta Kama ‘yan Kasar da suka fito zanga-zangar tsadar rayuwa da a gudanar a fadin Kasar a watan Augustan da ya gabata.
Sakataren yada labaran jam’iyyar Debo Olagunagba ya bayyana hakan a yau Litinin a yayin taron manema labarai a hedkwatar hukumar da ke Abuja.
Jam’iyyar ta ce yunwa da tsadar rayuwa ne suka dauki nauyin zanga zanga a Kasar ba wasu mutane ba.
Sakataren ya ce ya kamata gwamnatin Kasar ta mayar da hankali wajen magance yunwa, ba kama masu zanga-zanga ba.
PDP ta kara da cewa tsare-tsaren da shugaba Tinubu ya bijiro da su ne ya haifar da tsadar rayuwa da ake ci gaba da fuskanta a Kasar.
Jam’iyyar ta ce abin kunya da takaici ne yadda gwamnatin Tinubu ta sanya aka kama masu zanga-zangar, inda ta ce yunwa ya kama ta kama ba talakawa ba.
Jam’iyyar ta kara da cewa ya kama jam’iyyar APC ta hankalta da zanga-zangar da ‘yan Kasar suka yi wajen magance matsalolin Kasar.
Jam’iyyar na wannan kalamin ne bayan kama Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na Kasa NLC Joe Ajearo da jami’an DSS ta yi a yau Litinin.
‘Yan Kasar sun gudanar da zanga-zangar lumana ne a ranar 1 zuwa 10 ga watan Augusta, inda daga baya kuma ta rikide ta koma tarzoma.
Labarai
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Jami’an Lafiya Biyu A Kaduna
Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ma’aikatan jinya guda biyu mata, tare da marasa lafiya da dama, a lokacin da suka kai hari wani Asbiti da ke Kauyen Kuyallo a cikin karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.
Wani shugaban kungiyar ‘yan sa-kai a yankin da lamarin ya faru Musa Alhassan, ya bayyana cewa tun da fari bayan zuwan maharan sun fara nufar wata makarantar sakandiren gwamnati ne a yau Litinin da misalin karfe 9 safe da nufin yin garkuwa da daliban makarantar.
Acewar Musa bayan zuwan ‘yan bindigar makarantar suka tarar da babu kowa hakan ya sanya suka nufi Asibitin suka sace mutanen.
Musa ya ce ya zuwa yanzu ba a san adadi marasa lafiyar maharan suka sace ba a Asibitin.
Labarai
DSS Ta Kai Sumame Ofishi SERAP Na Abuja
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kai sumame ofishin kungiyar SERAP mai rajin kare tattalin arzikin Najeriya da ke Abuja.
Jami’an na DSS sun kai sumame ofishin ne sa’o’i kadan bayan da DSS din ta kama shugaban kungiyar kwadago ta Kasa NLC Jeo Ajaoro a yau Litinin a filin jiragen sama na birnin a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Kasar Birtaniya don halartar taron ‘yan kasuwa wanda za a gudanar a yau.
Sai dai bayan kama Ajerao, a wata wallafa da SERAP ta yi a shafin ta X, ta bayyana cewa, jami’an DSS sun kai’wa ofishinta na Abuja sumame, inda suka bayyana cewa su na neman daraktan kungiyar ne.
SERAP ta ce mamaye ofishinta da DSS suka yi sun yi ne ba bisa ka’ida ba, inda ta bukaci shugaba Tinubu da ya gargadi jam’an na DSS da su daina yin barazana ga mutane da kuma yin barazana ga ‘yancin ‘yan Kasar.
Kai sumame ofishin na SERAP na zuwa ne kwana guda da kungiyar ta bai’wa shugaban Tinubu wa’adin sa’o’i 48 da ya umarci kamfanin mai na Kasa NNPCL da ya janye karin farashin man da ya yi a Kasar.
-
Labarai7 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari