Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin daɗinsa bisa umarnin da ƙungiyar dattawan arewa sukai ga fulani da su ƙauracewa kudancin ƙasar.

Muhammadu Buhari ya ce hakan sam ba daidai bane kuma babu inda kundin tsarin mulki ya bawa wata ƙungiya dama da ta yanke wannan ɗanyen hukunci.
Cikin sanarwar da Mallam Garba Shehu ya fitar ya ce kamata yayi kowanne ɗan Najeriya ya kasance mai neman hanyar kawo zaman lafya kamar yadda gwamnatin ke fafutukar yi a halin yanzu, don shawo kan rikicin fulani da manoma.

