Jami’an yan sanda a jihar kano sun cafke wani Mutum mai shekaru 57 mai suna Tijjani Yahaya mazaunin unguwar Kofar Ruwa dake karamar hukumar Dala, bisa zarginsa da cakawa kaninsa Aminu Wuka Wanda yayi sanadiyar Mutuwarsa.

Dsp Abdullahi Haruna shine kakakin Rundunar yansandar jihar kano ya tabbatar da faruwar Al’amarin inda yace wanda aka cakawa Aminu ya rasu ne a Asibitin kwararru na Murtala .
Dsp Abdullahi ya kuma bayyana cewa an kama Wanda ake zargin da wuka a hannunsa.
Tuni dai Kwamishinan yansandar jihar kano Ahmad Ilyas ya bada umarnin Mika shi ga sashen binciken manyan Laifuka na Rundunar.

