Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje nuna damuwarsa matuka yadda ake nuna kyama akan Fulani makiyaya a kasar Nan.

Gwamnan ya kuma yi Kira ga gwamnatin Tarayya kan shirinta na Gina Rugage, da kada ta tabbatar da Shirin a yankunan da bana fulanin asali ba.

Haka zalika dakatar Shirin da gwamnatin Tarayya tayi bai dace ba kamata yayi ya zama zabi ne ga jihohi.

Gwamnan na wannan furuci ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a jihar sokoto, Jim kadan bayan kammala daurin Auren dan Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar Dattawar kasarnan.

A cewar gwamnan dakatar da Shirin da gwamnatin Tarayya tayi, ba haka ya dace ba kamata yayi a Gina Rugagen inda akasarin fulani ke zama a Yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: