Kungiyar Dakarun wucen gadi na Tsaftar Muhalli a jihar Kano sun Bukaci Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da ya cika musu Alkawarin Tabbatar dasu a matsayin cikakkaun Ma’aikatan tsaftar Muhalli.

Shugaban kungiyar Dakarun Abba Umar Gano ne yayi wannan Kira a lokacin da suka kawo ziyara Ofishin Mujallar Matashiya.
Ta Bakin Sakataren Kungiyar Mubarak Musa, inda ya tunatar da gwamnan Kano game da Alkawarin da yayi Musu na tabbatar dasu a matsayin Cikakkun Ma’aikan Tsaftar jihar Kano.

A cewar Mubarak Dakarun Tsaftar Muhalli sun kai 1000 ne Wanda suka fito Daga kananan Hukumomi 44 na jihar Kano.

Ya kuma kara da cewa Suna Mika koke ga gwamnati da hukumomi da A kafa musu hukumar zasu ci gashin kansu tare da tabbatar dasu a matsayin Cikakkun Ma’aikatan tsafta,
kamar yadda aka kirkiri Hukumar Karota a jihar Kano don ganin an tabbatar da Tsaftar Muhalli a fadin jihar Kano.
A cewarsa suna ta bibiyar hanyoyin da hakan zai tabbata amma har yanzu basu samu damar hakan ba wannan yasa suka soma amfani da kafafen yada labarai don sakonsu su ya isa ga Adalin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Ku tai makawa DAKARUN TSAFTA wajenbisar da sakon su ga gwamnati yaran suna kokari wajen dakile yaduwar cututtuka