Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran jiha

SAHAD STORE SUN SALLAMI MA’AIKATA 74 SAKAMAKON BATAN MILIYAN 25

Katafaren shagon siyar da kayayyaki daban daban mai Suna SAHAD store ya Sallami Ma’aikatan ta guda 74 a jihar Kano.

Sallamar Ma’aikatan ya biyo bayan batan wasu makudan kudade Har naira Miliyan 25 a tsakanin rassan shagunan guda biyu na kan Titin gidan Zoo da kuma na Unguwar Mandawari.

Shugaban Rukunin shagunan Alhaji Ibrahim Mijinyawa ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust lamarin na sallamar Ma’aikatan su, inda sakamakon batan wasu kudade na cinikin da akayi a bikin karamar Sallah.

Sai dai Al’umma na Alakanta korar Ma’aikatan a matsayin rashin Adalci, saboda Mafi akasarin Wanda aka kora basu da hannu ko masaniya a batan kudaden.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: