Farfesa Dahiru Yahya ne yayi Kira da mabiya sheikh Ibrahim Zakzaky da su cigaba da gudanar da zanga- zanga har sai an sako jagoransu.

Farfesan Wanda yake masani ne a fannin Ilimin Tarihi, yayi watsi da yadda gwamnatin Tarayya ta Kira mabiya Shi’a a matsayin yan Ta’adda.
A zantawarsa da manema labarai Farfesa yace yan Shi’a zasu cigaba da gudanar da zanga-zanga har sai an sako musu jagoransu da matarsa Zeenatu.

Ya kuma ce su cigaba da gudanar da dukkannin Al’amuran da suka saba yi na Shi’a kamar yadda aka saba, haka zalika Zanga-zangar da suke bai saba dokar kundin mulkin kasarnan ba.
