Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jihar ta shafe sama da watanni 60 ba tare da samun Rahoton Bullar Cutan Shan Inna ba.

Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da Karin kwanaki Gudanar da Allurar Rigakafin Polio da ya gudana a karamar hukumar Gezawa.
Gwamnan kanon Wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Dr Nasiru Yusif Gawuna ya bayyana irin kokarin masu zartawa a fannin lafiya, Wanda ya basu nasara da jajircewa da suka yi wajen bayar da Allurar Rigakafin Shan Inna.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa a shirye suke don Tabbatar da samar da ingantaccen kulawa a fannin lafiya a kananan hukumomi 44 a fadin jihar.
