An bayyana Sada zumunta a tsakanin Mutane Abu ne da yake kara tsawon Rayuwa a duniya musamman ayi shi saboda Allah.

Dr Ashir Tukur Inuwa shina ya bayyana hakan a yayin Taron kungiyar tsofaffin daliban koyon aikin jarida dake kwalejin Shari’a ta Aminu kano aji na 2013.
Ya bayyana muhimmancin zumunci musamman sada zumunta musamman a tsakanin dalibai.

Haka zalika ya yabawa wa kungiyar aji na 2013 a matsayin zakaran gwajin dafi wajen sada zumunta musamman yadda suka kulla auratayya a tsakanin maza da mata har sau Uku.

Shima a nasa jawabin Shugaban kungiyar tsofffin daliban aji na 2013 Yahaya Dahiru Aikawa, ya bayyana makasudin shirya Taron inda yace dama duk shekara anayi to amma na wanna lokaci anyi shi ne don nuna Farin cikin samun shaidar digirin digir gir da daya daga cikin malamansu ya samu wato Dr Ashir Tukur Inuwa.
Haka zalika Aikawa ya bayyana Alhininsa da tare da Mika jaje a madadin daukacin tsofaffin Daliban aikin jarida Aji na 2013, kan rasuwar Mahaifiyar malam Nasir Sadiq Ahmad.
Taron dai ya samu halartar daliban da dama maza da mata dama Wasu daga cikin malamansu Wato Malam Aminu Kabara.