Connect with us

Labaran ƙasa

Babban aikin dake Gaban Sabbin Ministoci shine Kawar da Talauci a tsakanin Yan Najeriya– APC

Published

on

Babban muhimmin aiki da ke gaban ministoci a hali, Yanzu da ake son su aiwatar shine fitar da yan Najeriya daga kangin Talauci, da tabbatar da tsaron rayukansu da dukiyoyinsu sai uwa uba bunkasa tattalin arzikin kasa.

Jam’iyar ta bayyana hakan ne ta cikin wani sakon taya murna da ta aikewa Ministocin, wacce Sakataren yada labarai na Jam’iyyar na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ya sanyawa hannu,inda jami’ar APC ta bukaci sabbin Ministocin da su nutsu sosai su kuma gudanar da ayyukansu yanda ya kamata.

Sanarwar ta kara da cewa, sabbin Ministocin da su tabbatar da nuna hali na gari bisa amincewar da Shugaban kasa tare da sauran yan Nijeriya suka yi musu ta hanyar zabar su don gudanar da ayyukansu a cikin hanzari domin tallafawa nasarorin da aka samu a sassa daban-daban Najeriya.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran ƙasa

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Miliyan 999 A Kullum Wajan Ciyar Da Ɗaliban Firamare

Published

on

Gwamnatin Tarayya, a ranar Talata, ta ce za ta kashe Naira miliyan 999 a kullum don ciyar da ɗalibai kusan miliyan 10 a shirin ciyar da makarantu na ƙasa a faɗin ƙasar nan.

Shugabar ƙungiyar NHGSFP, Aishatu Digil, ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki kan hanyoyin raba ku6daden don duba farashin ciyar da abinci a cikin shirin a Abuja.

Ta ce ministar agajin jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban al’umma Sadiya Farouq ta samu amincewar kashe Naira 100 ga kowane mutum a kullum wajen ciyar da shirin.

Ta ce ɗalibai 9,990,862 daga firamare aji ɗaya zuwa uku a shirin yanzu za a ciyar da su da N100 a kullum na tsawon kwanaki 20 a cikin wata da6ya, wanda zai kai Naira miliyan 999,086,200 a kullum.

“Kafin wannan, muna ciyar da yaran makaranta Naira 70 ga kowane yaro, kowane abinci.

Hakan ya kasance tun 2016, amma Shugaban ƙasa ya amince da N100 na sake dubawa.

“Muna da dukkan masu ruwa da tsaki kamar Hukumar Abinci ta Duniya, Hukumar Ƙididdiga ta ƙasa, Hukumar Wayar da kan Jama’a ta ƙasa , Global Alliance for In Proved Nutrition, Ma’aikatun Noma, Ilimi da sauran su don yin shawarwari kan yadda za a raba kuɗaɗen.

Continue Reading

Labaran ƙasa

Kotu Ta Haramta Wa Gwamnoni Anfani Da Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi

Published

on

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da manyan lauyoyin jihohi 36 suka shigar a kan Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NFIU) kan aiwatar da ƙa’idojinta na sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Ƙa’idojin sun takaita adadin da za a iya cirewa daga asusun ƙananan hukumomi zuwa fiye da N500,000 a kullum.

Sai dai masu shigar da ƙara (Gwamnatocin Jihohi) sun yi zargin cewa ƙa’idojin sun saɓawa ƴancin cin gashin kan harkokin kuɗi na jihohi daban-daban kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Saidai Alkalin kotun, Inyang Ekwo, ya ce shari’ar ba ta da inganci.

A cikin ƙarar, babban Lauyan gwamnatin tarayya (AGF), NFIU da kun6giyar ma’aikatan ƙananan hukumomin Najeriya ne ake tuhuma.

Hukumar ta NFIU ta fitar da wasu ƙa’idoji a watan Mayun 2019 domin kare kai daga tasirin da gwamnatocin jihohi ke yi wajen gudanar da rabon ƙananan hukumomi na wata-wata.

Da yake yanke hukuncin, Mista Ekwo ya ce ma’anar ƙa’idojin NFIU shi ne sanya gaskiyar kuɗi a cikin hada-hadar gwamnati a matakin ƙananan hukumomi.

Mista Ekwo ya yarda da AGF cewa ta hanyar sashe na 23 (2) (a), sashe na 28 (2) da sashe na 31 na dokar NFIU, “ɓangarin ta na da ikon yin ƙa’idojin.”

Ƙa’idojin sun yi niyya ne don rage “lalacewar laifuffuka da ake samu ta hanyar fitar da kuɗaɗe daga asusun ƙananan hukumomi a faɗin Najeriya daga ranar 1 ga watan Yuni, 2019.

A ranar 2 ga Maris, lauyan gwamnatocin Jihohin, Omonsoya Popoola, ya ce gwamnatocin jihohin ba su da iko da Hukumar NFIU.

Mista Popoola ya shaida wa kotun cewa ta hanyar gudanar da asusun haɗin gwiwar ƙananan hukumomin jihar, jihohin suna bin dokokin da Majalisar Dokoki ta Jiha ta kafa ba hukumar NFIU ba.

Ya buƙaci kotun da ta bayyana cewa NFIU ba ta da hurumin tsara ƙa’idoji da tsare-tsare da gudanar da asusun haɗin gwiwar ƙananan hukumomin jihar.

Sai dai AGF da Tijjani Gazali, Babban Lauyan Najeriya ya wakilta, ya ce NFIU ba ta kutsa kai cikin ikon jihohi ko ƙananan hukumomi.

“Babu wani abu da ba daidai ba ko sabawa kundin tsarin mulki game da ka’idodin NFIU saboda ba sa amfani da ikon masu shigar da ƙara,” Mista Gazali, daraktan riko na ƙararrakin jama’a a ma’aikatar shari’a ta tarayya, Abuja, ya shaida wa kotu.

Mista Gazali ya ƙara da cewa “a bayyane yake daga tanade-tanaden Dokar NFIU, musamman Sashe na 23 (2) (a) da Sashe na 28 (2) da Sashe na 31 na Dokar NFIU, cewa sashin yana da ikon yin jagororin. ”

Hakazalika, lauyan NFIU, Arthur Okafor, wanda shi ma SAN ne, ya ce hukumar ta yi aiki ne bisa ga hurumin da doka ta ƙayyade don hana cin zarafin ofis da sauran laifukan kuɗi da ka iya tasowa a matakin ƙananan hukumomi.

Continue Reading

Labaran ƙasa

​Shugaban Masu Kula Da Iyakokin Ruwan Nijeriya Dr bashir jamoh Yayi Awon Gaba Da Tiriliyan Ɗaya

Published

on

Dr. Bashir Yusuf Jamoh, shugaban NIMASA, ma’ana “Drecotor of Nigerian Maritime Administration and safety Egency” ta Nijeriya, Wanda shugaba Muhammadu buhari ya naɗa, an samu wasu rahotonni da suke nuni da cewa yayi handama da babakere na naira tiriliyan ɗaya da dubu Ɗari biyar.”

Biyo bayan wani bincike da hukumomin ƙungiyar yaƙi da cin hanci na ƙasar Amurka tayi, cikin asusun shi bashir Jamoh ɗin, binciken ya tababtar da waɗannan kazaman kuɗaɗen da aka tadda ciki shinfiɗe.”

Wani rahoto ya bayyana ire-iren aringizon haɗakar lambobin wasu asusun shi Jamoh ɗin tare da sauran bayanansa, da babban bankin ƙasar amurka ɗin ta bankaɗo a domin tabbatar da hujjoji, duba ga yadda acan ƙasar Amurka ɗin ya ajiye waɗannan maƙudan kuɗaɗen.”

Bayanan asusun Jamoh ɗin, da yayi amfani dasu na wurin wasa da hankalin gwamnati, a domin gujewa ɗayan bayanan asusun na shi da gwamnatin ta sanshi da shi, sune kamar haka:

Bayanan bankin da aka sankame waɗannan maƙudan sune kamar haka.

Banki: Fedility Banka, bayanin asusun 2215187650.

Suna Hamza Ibrahim Jamoh, tare da lambar akwatin tafi da gidansa na salula da yake amfani da shi na jiyo sako shine kamar haka, 08034517410, tare da sirrin BVN 2215837650.

Bugu da ƙari, biyo bayan bankaɗo waɗannan bayanan awon gaba da maƙudan kuɗaɗen da aka gano shi, daga bisani an tabbatar cewa, bayanan sun shiga hannu ƙarƙashin hukuma zirga-zirga ta Nijeriya wato NPA, ita hukumar ta tabbatar da wannan badaƙalar wawuson da Jamoh yayi.

Global Investigators United Kingdom, ita ta ƙaddamar da wannan binciken kan badaƙalar kuɗi naira tiriliyan ɗaya da dubu Dari biyar da Jamoh ya wawushe daga nan gida Nijeriya zuwa ƙasar Amurka.”

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: