Iran, Saudia Sun Kama Hanyar Rusa Arewa

Babu shakka ga duk mai bibiyar irin muhawarori da ake tafkawa a kafofin sada zumunta na zamani, musamman a nan Arewacin Najeriya zai fahimci yadda ake zazzafar kazamar muhawara a tsakanin manyan bangarori biyu wanda idan ka bisu a hankali sai ka fahimci duka tushen da suka tsiro yana tikewa ne ga turbar siyasa ta kasashen Saudi Arabia da kuma kasar Iran, yana da matukar wahala mutum ya iya fahimtar hakan a lokaci guda, kasancewar yadda siyasar wadannan kasashe tayi tasiri da sunan addini, wanda mu kuma a Arewa duk abinda aka jinginashi da addini zai wuya jama’a su fahimci illarsa.

Matasa sune ke nuna halin da al’umma zata kasance a gaba, kafin wannan rubutun na bibiyi zauruka da dama musamman a Facebook da kuma WhatsApp wadda na ganewa idona yadda matasa da dama tunaninsu ya juye matuka, daga tunanin kawowa al’ummar mu cigaba, zuwa tunanin kare muradun siyasar wadannan kasashe, wanda dukkansu siyasa ce suke sai dai kawai wasu sunfi wasu iya taku.

Kasancewar da yawa daga matasan mu basu da ‘yancin yin tunani sai-dai ayi musu, wanda zaku fahimci hakan a kwanakin baya lokacin da akace wata mawakiya zataje kasar Saudi Arabia don gudanar da wasanta na nishadi, wanda bai da alaka da musulunci, tunda ba da sunan musulunci tace zataje ba, sai gashi masu bin siyasar kasar suna kokarin baiwa zuwan nata kariya da sunan larura ce, su kuma masu bin siyasar Iran suka fara sukarsu ta ko ina, ba wai don sun sabawa musulunci ba, sai don kawai a ga wallen kasar da ta sabawa kasar Iran.

Irin hakan ta faru a kwankin baya lokacin da alaka tayi tsamari, tsakanin kasar Iran da Amurka wadda ko kadan ba rigima ce ta addini ba, amma sai gashi masu goyon bayan siyasar Saudi Arabia suna goyon bayan Amurka, su kuma masu goyon bayan siyasar Iran suna goyon bayanta.

Shekaran jiya ina jin karatun Dr. Ahmad BUK a rediyo, sai naji yana bada labarin wasu shekaru a baya da kasata Najeriya tafi kasashen Saudi, Dubai da sauransu cigaba, wanda a yanzu ba haka abin yake ba.

Tabbas akwai bukatar matasan mu, su fahimci cewa maida hankali wajen siyasar wadancan kasashe, maimakon maida hankali kan cigaban kasarmu babu wani abu da zai tsinana mana sai koma baya.

Zan dakata a nan, don gudun tsawaitawa.

Basheer Sharfadi
04-09-2019.
#NigeriaFirst #Nigeria #SaudiArabia #Iran

One thought on “Ra’ayi: Iran, Saudia Sun Kama Hanyar Rusa Arewa -Sharfadi”
  1. Ni banaganin cewa wannan dalili ne Na cewa saudiya da Iran sun kama rusa arewa

    Domin rubutun da kayi ma baida alaka da kokarin wargaza arewa

    Wadanda suke sukan Zuwan mawaqiya suna suka ne saboda ganin girman Kasar aduniyar Musulunci, koda kuwa ita saudiya tana yiwa abun kallon shiyasa ne

    Kaga kenan mu ga kallon da mukeyi suma ga ganin da sukeyi, sannan kaima Sharfadi kasan kokarin bata tarbiyar musulmai da duniya takeson yi, kaga kenan ganin shiyasa baikamata ya hanamu hango Addinin mu ba

    Allah ya datar damu

Leave a Reply to Haruna Dan umma7 Cancel reply

%d bloggers like this: