Hukumar Hana fasa kauri ta Najeriya tayi dirar mikiya a wani Otal dake Birnin Tarayyar Abuja Mai suna Fraisier Suite.
Majiyar matashiya ta rawaito cewa jami’an Hukumar Custom sun rufe kofar Shiga Otal din tare da bincikar wasu motoci kimanin 11 dukkanin su kirar Toyota Lexus ne da Mercedes Benz, sai Kuma Toyota Prado. Da sauransu.
A cewer wani jami’in Custom yace dalilin zuwan su Otal din shine sun samu bayanan sirri na cewa Otal din ya zama mafakar motocin da basu samu lasisin shigowa ba daga hukumar ta Custom don haka Suka shigo don kama motocin tare da tafiya dasu.
Mutanen dake zaune a Otal din dai sun Kasance cikin barazana a lokacin da jamii Suka shigo.