A dai dai lokacin da Najeriya ke bikin murnar cika t59 da samun yancin kai daga hannun Turawar Mulkin mallaka, wata Kungiyar matasa masu hangen nesa a Najeriya wato Young Visionaries Association of Najeriya a Turance (YVAN) ta kai ziyara gidan masu Rangwamen hankali dake Dorayi, inda kai musu abubuwan da Suka fi bukata a gidan.

A cewar Shugaban kungiyar Reshen jihar kano Comrade Bashir Madara yace sai da Suka tuntubi mahukuntar gidan don jin irin abin da Suka fi bukata sune kamar Man shafawa, Omo na wanki da sabulun wanka sai kuma Maganin sauro.

Wannan yasa Suka yi kokari don ganin sun tallafa da irin nau’in abubuwan da Suka fi bukata, kuma Suka zabi wannan muhimmin Rana don sanya mutanen farin ciki a zukatansu ta hanyar tallafa musu.

Itama anata jawabin Shugaban gudanarwar gidan Hajiya Bilkisu Dayyab ta nuna farin ciki tare da godewa wannan kungiya inda tace tabbas idan irin wannnan kungiyoyin suna kawo irin wannnan tallafi to suna maraba dashi,
A cewar ta duk da gwamnati na kokari wajen sauke dukkannin bukatun wannan gida sai dai hakan bai hana su karbar gudunmawar kungiyoyi irin wannan ba.

Mai kula da shiyyar nan na kungiyar Najmudden Mukhtar yace wannan irin aiki ba shi bane karo na farko da Suka saba yi ba abaya sun kai tallafi Asibitin Yara na hasiya Bayero inda Suka tallafa musu da omo, sabulu da Pampers da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: