Rundunar yansandan jihar legas sun sake bankado wata Ma’aikatar cinikayyar Jarirai a unguwar Cele Bus Stop dake Oshodi Apapa.

Yansandan dai sun gano yan mata a gidan da basu wuce shekaru 13- 27 inda suke samun juna biyu daga bisani idan sun haife yaran sai a rika siyar dasu.

Kakakin Rundunar yansandan jihar legas Bala El-Kana ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace makon da ya gabata sun bankado wani gidan da ake irin wannan harkar tare da ceto mata19 dukkansu dauke da juna biyu sai gashi yau ma sun sake gano wani gidan tare da ceto wasu matan da juna biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: