A da banyi niyyar nayi magana ba Amma duba da yanayin da aka tsinci Kai a wannan lokacin na matsaloli tsakanin malaman jami’a da dalibansu to wannan al’amari da yake faruwa ba wai sabon lamari bane hakan yadade Yana faruwa atsakanin Al,ummarmu ta wannan zamani shin meyasa ba a bawa su matan laifi sai dai su malaman? Yakamata muringa yin adalci a tsakanin Al, ummarmu mafi yawancin faruwar wannan lamarin bacin Rana ke sa dubu tacika saboda Mata masu rauni sai aringa Goya musu baya? jama’a wallahi ba,a gyara barna da goyon bayan daya daga cikin masu laifi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba idan mace Bata bawa namiji hadin Kai ba tin Babu Wanda yaji ze fita harkarta yanemi dai dai da halinsa munga kenan da akwai amincewa daga bangaren matan yanzu a wannan zamanin rayuwar Mata ta lalace awannan zamanin ta duk inda ba,a tinani idon Mata ya rufe Akan son abin duniya iskanci yazama bakomai ba ne awajen wasu matan a da ne mace ke Jin kunya Akan aikata badala Amma yanzu yin hakan shine wayewa awajen wasu matan ayanzu yzm abin tutiya mace take lalata da wani babban mutum Koda kuwa bazai Bata komy ba Kuma wallahi mazan biya sukeyi Yana da kyau muringa duba na tsanaki da yin adalci atsakanin Al ummarmu idan wani lamari yafaru muke duba bangarori biyu bawai mu dubi bangaren daya ba muyita CeCe kuce akai muke duba natsanaki tahanyar nazari Akan dikkanin matsaloli da suka shafi Al, ummarmu ko mun Sami wasu hanyoyi na gyara rayuwar wadanda suka Bata acikinmu…ni mace ce Kuma ciwon ya mace na ya mace ne Kuma ni banyarda laifin lecturers bane domin Suma matan da nasu laifin saboda dalilai kamar haka:

1 Yaran mu Mata su suke zuwa ofisoshin malaman tahanyar anfani da wayar sasula domin cimma matsayar wajen haduwa

2 Mata su sukace amsawa da bakinsu sun amince da aikata lalata ayayin da akayimusu tayin aikatawa

3 Ana samun lalatattun matan da bakinsu su ke fadin iya adadin kudi ko Kuma wata matsaya amatsayin biya bayan kammala lalata

4.lokuta da dama Mata ke fara Jan hankalin maza tahanyar yin shigar banza da nuna tsaraicinsu ko Kuma fitar da wani sashi na jikinsu

5.matan sukan bijoroma da maza buqatar su domin cimma matsayar wata muhimmiyar buqatarsu idan ansamu akasi be cika alqawari b sai su tona asari tahanyar nuna su mutanen kirki ne namiji ne yafara nemansu su Kuma wasu wawaye daga cikin mutanen mu sai su Basu mafaka tahanyar Dora dikkanin laifin Akan namijin.

A karshe Ina Kira da maza da suji tsoron Allah su Kare martabar addinninsu da aikinsu ko babu komi alƙawari mutum ya daukarwa kasarsa zaiyi service da gaskiya Kuma kasani dik abinda shaidan yaqawata ma kayi da Yar wani haka za,a Yi da taka Yar ko da sanin ka ko babu saninka Allah ya shiryar da mu tafarki na gaskiya musulmin mu da kiristoci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: