Likitoci na Kokarin ceto wani yaro dan watanni 13 Mai suna Michael Duniya Wanda wani kare Mai suna PitBull yayi yunkurin Hallaka shi.

Abin dai ya faru ne da misalin karfe 7:30 na safiyar jiya a barikin Mambilla dake Abuja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Karen ya balle daga kejin da yake a rufe ne inda ya tarar da Michael na wasa nan take ya kai masa farmaki da kyar aka kwaci yaron a bakin Karen.

Daga bisani aka garzaya dashi asibi inda ake bashi kulawa ta musamman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: