Uwar gidan Shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari ta bayyana dalilanta na barin Najeriya na tsawon Watanni.

Aisha tace ta tafi kasar Ingila ne don duba lafiyarta daga bisani ta tafi kasar Spaniya don duba ‘yarta Zahra Buhari da haihu acan kasar.
Daga bisani na ziyarci kasar Saudiya, don gudanar da ibada.

Aisha Buhari ta bayyana hakan ne ga manema labarai Jim kadan bayan ta sauka a filin tashi da sauka na jiragen sama Na Nmamdi Azikwe dake Abuja.

Uwar gida Aisha tayi Kira da Yan Najeriya dasu guji yada labaran jita jita, ko kuma na karya musamman a kafafen sada zumunta.

Daga bisani ta godewa dinbin Yan Najeriya da suka taya ta addu’ion samun lafiya tare da dawo da ita gida lafiya, bayan ta karbi shawarwari daga bakin likitocin kasar Burtaniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: