Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kadu matuka da jin labarin mutuwar wata mata da yayanta sakamakon fashewar wani tankar dakon mai.

Motar ya fadi ne a kusa da wani asibiti mai suna Toronto dake unguwar Upper Iweka dake garin Onicha.
Matar da rasa ranta tayi Kokarin kaucewa afkawa hadarin Amma ina Bata samu daman tsallakewa ba sakamakon fadawa wani kwata da tayi da yayanta nan take suka mutu.

Muhammad Buhari ya jajantawa iyalan Wanda suka rasa ransu tare da tausayawa Wanda hadarin ya shafa musamman yadda akayi Asarar Dukiyoyi da rayuka.
