Hukumar da ke yaki da masu fasakaurin kaya(Customs)sun kama wani motar dakon Man fetir dauke da shinkafa buhu 250 a ciki.

Shugaban hukumar shiyyar Mai kula da jihar kano da jigawa Nasir Ahmad shine ya sanar da hakan ga manema labarai a yau.
Inda yace sun kame Babbar Tankar motar ne a hanyar daura inda yake Kokarin shigowa kano.

Nasir Ahmad yace wannan sabon hanyar fasa kaurin kaya abin tsoro ne saboda yadda Mai dakon mai zai iya daukar shinkafa sabida kudi ya bar dakon Mai, kenan zai iya dauko makamai ko kwayoyi a ciki.
Don haka jami’an sa bazasu zuba ido hakan na faruwa ba.

Idan ba’a manta ba Shugaban kasa Muhammad Buhari ya fada umarnin rufe iyakokin Najeriya ne don hana shigo da kayan kasashen waje da Abinci irin nau’in shinkafa ta iyakokin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: