Rahotanni daga cibiyar dake lura da cuttutuka ta kasa (NCDC) sun tabbatar bullar cutar Lassa a jihar Binuwai Wanda yayi sanadiyar mutuwar Mutane biyar (5).

Babbar ja mi’ar hukumar Dake lura da sashin sadarwa Hajiya Hannatu Bello itace ta shaida hakan ga manema labarai a birnin Makurdi yau.
Inda ta bayyana cewa sun samu rahotan mutane 21 ne suka kamu da cutar Lassa a jihar, inda bincike ya tabbatar da mutane 8 daga cikin 21 cutar ta musu illa, daga ciki kuma mutane 5 ne suka rasa ransu a yanzu haka.

Yanzu haka ragowar suna can Ana bincikar lafiyarsu tare da dakile yaduwar cutar a tsakanin Al’umma.

Photo/daily trust