Hukumar Hizbah a jihar Kano ta tabbatar da wasu mutane fiye da 20 waɗanda ke ɗauke da cutar ƙanjamau a cikin mutanen da hukumar ta kamo a wani samame da ta kai garin Bichi.

Aƙalla mutane 27 ne ciki fiye da 90 ke ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

A wani bincike da likitoci suka yi bisa kulawar hukumar Hizbah n tabbatar da mata 23 na ɗauke da cutar yayinda maza 4 suke ɗauke da ita.

Hukumar hizbah ta kai samamen ne ƙauyen Badume da ke ƙaramar hukumar bichi a Kano inda ta kamo mata masu zaman kansu da maza fiye da 90.

Leave a Reply

%d bloggers like this: