Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya sanata shehu sani yace yawan zirga zirga da Shugaban kasa Muhammad Buhari yakeyi abu ne da zai taimaki Al’ummar kasa wajen habbakar Tattalin Arziki da magance mataslar tsaro.

Shehu sani bayyana hakan a shafin sa na Twita inda yace Shi a ganinsa tafiye tafiyen da yake yawan yi a Yan kwanakin nan abu ne da zai kawo cigaba a fadin kasa dama Al’ummar Najeriya.
Wannan kalaman shehu sani ya biyo bayan korafe- korafe da wasu ke yi na yawan tafiye tafiye da Shugaban kasa keyi a Yan kwanakin nan.

Yanzu haka Shugaban kasa Muhammad Buhari yana kasar Saudiya don halattar Habbakar Tattalin Arziki inda ya tafi a jiya litinin bayan ya dawo daga Kasar Rasha kasa da Awanni 48
