Gwamnatin jihar Kano ta kammala wasu rijiyoyin samar da ruwan sha masu amfani da hasken Rana a dajin Ɗanshoshiya da ke ƙaramar hukumar ƙiru.

Aikin da aka gudanar ta bangaren ma aikatar samar da ruwan sha ta jihar Kano, babban sakataren ma aikatar Alhaji Auwalu Iliyasu Riruwai ya tabbatar da samun nasarar aikin makwanni kaɗan da ƙaddamar da shirin.

Cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yaɗa labaran Gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya aikewa mujallar Matashiya, sanarwar ta ce cikin gidaje 200 da gwamnatin ta ɗauki ɗamarar samarwa fulani, tuni aka fara wasu daga ciki, wanda zai ɗauki ɗakunan kwana da banɗaki da kuma ɗakin girki.

Idan ba a manta ba, gwamnatin Kano ta ɗauki alƙawarin hakan ne don magance yawan rikici tsakanin fulani da makiyaya a wani ɓangaren kuma a shigo da su don basu dama a matsayinsu na ƴan ƙasa.