Gwamnatin jihar legas ta gano wani gida da aka ajjiye Dan Zaki Mai shekaru biyu a matsayin Mai gadin gidan.

Shugaban dake samar da kudin shiga ta hanyar muhalli Mr Yinka Egbeyemi shine ya shaida hakan ga manema labarai a jiya lahadi.
A cewar yinka sun gano gidan ne Mai lamba 229 a unguwar Muri Okunola daka Yankin Victoria Island.

An dai gano mazauna gidan Yan asalin kasar Indiya ne, jnda a yau Litinin za’a dauke zakin don mayar dashi gidan adana dabbobi na jihar.
