Kwana ɗaya tak da jami an ƴan sanda suka kama wanda ake zargi ya kaɗe ɗan Karota har ya rasa ransa, a yammacin asabar direban wata tirela ya kuma bi ta kan wani inda jami in Karotan ya rasa ransa.
Cikin sanarwar da jami in hulɗa da jama na hukumar Nabulusi Abubakar ƙofar Na isa ya fitar a safiyar yau, ya ce tuni jami ansu da haɗin kan jama ar wajen suka kama wanda ake zargi sannan suka miƙashi ga jami an ƴan sanda mafi kusa.
Lamarin ya faru a unguwar Hotoro NNPC, kuma tuni marigayi Abdurrahmad ya rasa ransa.
Shugaban hukumar kula da tuƙi a jihar Kano Baffa Babba ya aike da saƙon ta aziyya ga iyalan mamacin.