Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da shirinta na kakkaɓe ɓata gari a yayin gangamin Maukibi a Kano.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce dakarunsu na sane da waɗanda ke amfani da taro don yin sata, kwace, da kuma tada hankali.

Ya ce ba za su zuba ido a kan hakan ba sai sun tabbatar sun magance matsalar.

Sanarwar da ya fitar a madadin kwamishinan ƴan sanda Habu A Sani, DSP Abdullahi Kiyawa ya ja hankalin al umma da su bada rahoton duk wata tarzoma ko wani lamari da ba su aminta dashi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: